INEC za ta dauki mataki kan ’yan takara masu saba dokar zaɓe bayan hukuncin kotun koli

0
INEC za ta dauki mataki kan ’yan takara masu saba dokar zaɓe bayan hukuncin kotun koli

INEC za ta fitar da sabbin bayanai kan shirye-shiryen zaben 2027 da ya rage kwanaki 100

Spread the love

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa za ta fara ɗaukar mataki kan ’yan takarar da aka samu sun karya tanade-tanaden dokar zaɓe, bayan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke kan wasu sassa na Dokar Zaɓe ta 2026.

Kotun Ƙolin ta dawo da wasu muhimman tanade-tanade guda huɗu, wato sashe na 77(5), 77(6), 77(7) da 84(2), waɗanda suka shafi rajistar ’yan jam’iyya da kuma yadda jam’iyyu ke zaɓar ko gabatar da ’yan takararsu. Hukuncin ya soke hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke a baya kan waɗannan tanade-tanade.

Rahotanni sun ce hukuncin na iya shafar wasu ’yan takara da tsarin zaɓen fitar da gwani da jam’iyyu suka gudanar, musamman wajen bin ƙa’idojin rajistar mambobin jam’iyya da kuma hanyoyin gabatar da ’yan takara. Sai dai hukuncin Kotun Ƙolin bai ce kai tsaye dukkan zaɓen fitar da gwanin da aka riga aka gudanar ya zama ba bisa ka’ida ba.

INEC na fuskantar aikin tantance yadda za a aiwatar da hukuncin kafin fara ɗaukar mataki kan waɗanda za a samu sun saba wa dokar.

Wannan matakin na zuwa ne yayin da shirye-shiryen zaɓen 2027 ke ƙara ƙamari, kuma hukuncin Kotun Ƙolin na iya haifar da sabbin ƙalubale ga wasu jam’iyyu da ’yan takararsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *