Ina son Atiku ya tuna lokacin da ya nemi tallafin Tinubu bayan rikicinsa da Obasanjo – Shettima

0
Atiku ya nemi tallafin Tinubu bayan rikicinsa da Obasanjo - Shettima

Atiku ya nemi tallafin Tinubu bayan rikicinsa da Obasanjo - Shettima

Spread the love

Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Sanata Kashim Shettima, ya caccaki tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, kan rikicinsa da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, inda ya yi zargin cewa Atiku ya nemi taimakon Shugaba Bola Ahmed Tinubu a lokacin da ya samu matsala a jam’iyyar PDP.

Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, yayin bikin ƙaddamar da kamfen ɗin jam’iyyar APC a jihar Kaduna, gabanin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Shettima ya ce lokacin da Atiku ya fuskanci matsin lamba da matsalolin siyasa a PDP, har ya rasa matsugunin siyasa, ya garzaya wajen Tinubu, wanda a lokacin yake gwamnan jihar Legas, domin neman goyon baya da mafita.

A cewar mataimakin shugaban ƙasar, Tinubu ya taimaka wa Atiku ta hanyar ba shi damar amfani da dandalin siyasa na jam’iyyar Action Congress (AC) domin tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2007, bayan rikicin da ya shiga tsakaninsa da Obasanjo.

Shettima ya bayyana cewa bai dace Atiku ya manta da irin wannan taimako ba, har yanzu yana neman ƙalubalantar Tinubu a zaɓen 2027.

Shettima ya jaddada cewa Shugaba Tinubu ya cancanci kammala wa’adin mulkinsa, yana mai amfani da tarihin dangantakar siyasa tsakanin shugabannin biyu wajen sukar burin Atiku na komawa fadar shugaban ƙasa.

Sai dai kalaman nasa sun sake buɗe sabon babi na muhawarar siyasa tsakanin APC da Atiku, wanda yanzu yake neman shugabancin ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar ADC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *