Gwamnatin Sokoto ta yi watsi da korafin ADC kan naɗin Kwamishinan INEC
Gwamnatin Sokoto ta yi watsi da korafin ADC kan naɗin Kwamishinan INEC
Gwamnatin Jihar Sokoto ta yi watsi da ƙorafin ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar ADC, Honarabul Manir Muhammad Dan’iya, kan naɗin Farfesa Mustapha Aliyu a matsayin Kwamishinan Ƙasa na Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), mai wakiltar Arewa maso Yamma.
Mai ba Gwamna Ahmed Aliyu shawara kan harkokin siyasa, Honarabul Faruku Labbo, ne ya bayyana hakan, inda ya ce an naɗa Farfesa Mustapha ne bisa cancanta da ƙwarewarsa.
Ya kuma ƙalubalanci Dan’iya da ya gabatar da hujjojin da za su tabbatar da zargin da yake yi.
A baya, Dan’iya ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sake duba naɗin, tare da kira ga Majalisar Dattawa da ta gudanar da cikakken bincike kan cancantar wanda aka naɗa.
Ya bayyana damuwarsa kan alaƙar zumunci tsakanin Farfesa Mustapha Aliyu da Gwamna Ahmed Aliyu, yana mai nuna shakku kan yiwuwar nuna bambancin siyasa a aikinsa.
Sai dai Labbo ya jaddada cewa alaƙar iyali kaɗai ba ta isa ta hana mutum riƙe muƙami ba, yana mai cewa ya kamata a yi la’akari da ƙwarewa da cancantar Farfesa Mustapha Aliyu.
Ya kuma buƙaci Majalisar Dattawa da jama’a su tabbatar an tantance wanda aka naɗa bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma ikonsa na gudanar da aikinsa cikin adalci da rashin nuna bambancin siyasa.
