El-Rufai ya isa kotu a Kaduna domin ci gaba da shari’arsa
El-Rufai ya isa kotu a Kaduna domin ci gaba da shari’arsa
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya isa Babbar Kotun Jihar Kaduna a ranar Talata domin ci gaba da sauraron shari’ar da ake yi masa kan zargin rashawa da wasu laifuffukan kuɗi.
El-Rufai ya isa kotun ne bayan Mai Shari’a Darius Khobo ya umarci Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifuffuka Masu Alaƙa da Hakan (ICPC) da ta gurfanar da shi a gaban kotu, bayan rashin zuwansa zaman shari’ar da aka yi ranar Litinin.
Rahotanni sun ce zaman na ranar Talata ya biyo bayan dage shari’ar, bayan da aka sanar da kotun cewa tsohon gwamnan ya nemi ganin likitansa domin duba sakamakon wasu gwaje-gwajen lafiya.
Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Kaduna ta yi watsi da ƙarar da ya ɗaukaka kan ƙin bayar da belinsa.
Ana tuhumar El-Rufai da zarge-zargen da suka haɗa da zamba, almundahanar kuɗi da amfani da muƙami ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda ake dangantawa da lokacin da ya jagoranci jihar daga 2015 zuwa 2023.
Sai dai tsohon gwamnan ya musanta aikata laifi, kuma har yanzu zarge-zargen na jiran hukuncin kotu.
