Ba za a iya kawo karshen ‘yan bindiga da ayyukan soji kawai ba – Ribadu
’Yan ta’adda na amfani da Social Media da kuɗaɗen Kirifto wajen tallafa wa ta'addanci - Ribadu
Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa ba za a iya kawo ƙarshen ayyukan ’yan bindiga a Najeriya ta hanyar amfani da ƙarfin soji kaɗai ba.
Ya ce akwai buƙatar haɗa ƙarfafa tattara bayanan sirri, tsaron iyakoki da sa hannun al’umma domin shawo kan matsalar rashin tsaro.
Ribadu, wanda daraktan harkokin shari’a a ofishinsa, Zakari Mijinyawa, ya wakilta, ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa kan hanyoyin magance matsalar ’yan bindiga da aka gudanar a Sakkwato.
Ya ce ayyukan ’yan bindiga sun wuce satar shanu, fashi da garkuwa da mutane, inda yanzu suka haɗa da mamaye yankuna, karɓar haraji ba bisa ƙa’ida ba da kuma kawo cikas ga harkokin tattalin arziki.
Ya ƙara da cewa kusancin Jihar Sakkwato da Jamhuriyar Nijar da yankin Sahel na bai wa ’yan bindiga damar tsallaka iyakoki da ci gaba da aikata laifuffuka.
Saboda haka, ya buƙaci hukumomin tsaro su ƙara haɗin gwiwa wajen musayar bayanan sirri, hana safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba, da kuma ƙarfafa tsarin gargaɗin al’umma tun da wuri.
Ribadu ya kuma jaddada muhimmancin samar da ayyukan yi da damar ci gaban tattalin arziki ga matasa domin hana shigar da su cikin ƙungiyoyin masu aikata laifuffuka.
Ya ce nasarar yaƙi da rashin tsaro ba za ta tsaya ga kama mutane ko ƙwato makamai ba, sai an tabbatar da cewa mazauna yankunan da rikici ya shafa sun koma gidajensu, manoma sun koma gonakinsu, makarantu sun buɗe, kasuwanni sun farfaɗo, kuma jama’a sun sake samun kwanciyar hankali.
