Atiku ya bukaci INEC ta bayyana kamfanonin da za su buga kayan zaɓen 2027
Atiku ya bukaci INEC ta bayyana kamfanonin da za su buga kayan zaɓen 2027
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana sunayen kamfanonin da aka bai wa kwangilar buga muhimman kayayyakin zaɓen 2027, domin tabbatar da gaskiya da amincewar jama’a kan shirin gudanar da zaɓen.
Atiku, wanda yake takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, ya kuma nemi hukumar ta yi bayani kan sauye-sauyen da aka yi wa wasu manyan jami’anta a sassa masu muhimmanci, musamman sashen gudanar da zaɓe.
Ya ce ya kamata INEC ta bayyana dalilan sauye-sauyen da kuma ƙa’idojin da aka bi wajen naɗa jami’an.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma buƙaci INEC ta tabbatar ko ta musanta rahotannin da ke cewa kamfanin Hitech ko wani kamfani mai alaƙa da shi ya samu kwangilar buga kayayyakin zaɓen da suka haɗa da takardun ƙuri’a.
Ya kuma nuna damuwa kan rahotannin cewa wani kamfani da ba a bayyana sunansa ba zai iya buga fiye da rabin muhimman kayayyakin zaɓen, yayin da kamfanin buga takardun kuɗi na Najeriya (NSPMC) zai kula da wasu jihohi kaɗai.
Atiku ya jaddada cewa INEC ta bayyana sunayen kamfanonin da suka samu kwangilolin, kuɗin kwangilolin, yadda aka ba da su da kuma matakan tsaro da za a bi wajen buga, adanawa da rarraba kayayyakin zaɓen.
Ya ce jam’iyyar ADC za ta sa ido kan shirye-shiryen zaɓen tare da sanar da masu sa ido na cikin gida da na ƙasashen waje duk wani abu da take ganin bai dace ba, yana mai cewa gaskiya da adalci su ne ginshiƙan amincewar jama’a ga zaɓen 2027.
