Atiku bai da ƙwarewar yadda za’a gudanar da tattalin arziki na zamani – Shettima

0
Atiku ya bai da ƙwarewar gudanar da tattalin arzikin zamani - Shettima

Atiku ya bai da ƙwarewar gudanar da tattalin arzikin zamani - Shettima

Spread the love

Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya soki tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, yana mai cewa bai da ƙwarewar da ake buƙata wajen tafiyar da tattalin arzikin zamani.

Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin taron koli na tattalin arzikin Najeriya karo na 32 da aka gudanar a Abuja.

Shettima ya yi wannan furuci ne yayin da yake sukar shawarar Atiku ta dawo da tallafin man fetur idan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Ya bayyana shawarar a matsayin yunƙurin mayar da Najeriya baya domin cimma muradin siyasa, yana mai cewa hakan na iya ƙara jefa ƙasar cikin talauci.

Shettima ya kuma bayyana cewar tarihin karatunsa bai nuna yana da ƙwarewar da ake buƙata wajen gudanar da tattalin arzikin zamani ba.

Shettima ya buƙaci ’yan Najeriya su yi la’akari da ƙwarewa da manufofin ’yan takara kafin yanke shawarar wanda za su zaɓa.

Sai dai Shettima ya kare matakin Shugaba Bola Tinubu na cire tallafin man fetur, yana mai cewa shugaban ƙasar ya ɗauki matakin ne saboda fahimtar halin da tattalin arzikin Najeriya yake ciki.

Batun tallafin man fetur na ci gaba da zama ɗaya daga cikin manyan batutuwan da ake takaddama a kansu tsakanin gwamnatin APC da ’yan adawa gabanin zaɓen 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *