Wata mata mai shekara 18 ta caka wa mijinta wuka a Bauchi bayan rigima kan kuɗi

0
Wata mata mai shekara 18 ta caka wa mijinta wuka a Bauchi bayan rigima kan kuɗi

Wata mata mai shekara 18 ta caka wa mijinta wuka a Bauchi bayan rigima kan kuɗi

Spread the love

Wata mata mai shekara 18, Fatima Dalha, ta shiga hannun ‘yan sanda bisa zargin caka wa mijinta mai shekara 30 wuka a cikinsa, sakamakon wata saɓani da ya ɓarke tsakaninsu kan kuɗi da wasu kayayyakin amfanin gida a Jihar Bauchi.

Lamarin ya faru ne a yankin Lirr Bajar da ke ƙaramar hukumar Dass, da misalin ƙarfe 6 na safiyar Lahadi, 25 ga Oktoba, 2026.

Rahoton ya bayyana cewa ma’auratan sun samu saɓani ne kan kuɗi, da kuma wata wayar hannu da matar ta yi ikirarin mallakarta ce.

Ana zargin cewa saɓanin ya ƙazance har ya rikide zuwa faɗa, inda Fatima ta ɗauki wuƙa ta caka wa mijinta a ciki.

Bayan faruwar lamarin, jami’an ‘yan sanda na sashen Dass sun garzaya wurin, inda suka kai wanda aka raunata zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci.

A halin yanzu, mijin na ci gaba da karɓar magani, yayin da ‘yan sanda suka kama matar tare da ƙwato wuƙar da ake zargin an yi amfani da ita wajen aikata laifin.

Rahoton ya kuma bayyana cewa wasu fusatattun mutane sun yi ƙoƙarin halaka matar kafin jami’an tsaro su kai ɗauki tare da kuɓutar da ita.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya nuna damuwarsa kan yadda rikicin cikin gida ke ƙara faruwa tsakanin ma’aurata matasa, inda ya shawarci ma’aurata da su riƙa warware saɓani cikin lumana ta hanyar neman taimakon iyalai, dattawa da kuma bin hanyoyin da doka ta tanada.

Ya kuma yi gargaɗi ga jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu, yana mai tabbatar da cewa za a gudanar da cikakken bincike kan lamarin kafin ɗaukar matakin da ya dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *