Kotu a Adamawa ta yanke wa uba da ya yi wa ‘yarsa ciki hukuncin daurin shekaru 30
Kotu a Adamawa ta yanke wa uba da ya yi wa 'yarsa ciki hukuncin daurin shekaru 30
Wata Babbar Kotun Upper Area da ke Ganye a Jihar Adamawa ta yanke wa wani mutum mai suna Jediel Sylvester hukuncin daurin shekaru 30 a gidan yari bayan samunsa da laifin yi wa ‘yarsa ta cikinsa ciki.
Kotun ta bayyana cewa mutumin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, lamarin da ya janyo yanke masa hukunci mai tsauri domin nuna cewa ba za a lamunci irin wannan mummunan laifi ba.
Alkalin kotun ya ce hukuncin zai zama darasi ga masu aikata laifukan cin zarafin yara da kuma kare martaba da haƙƙin yara a cikin al’umma.
Lamarin ya tayar da hankalin jama’a a Adamawa, inda masu rajin kare haƙƙin yara suka yi maraba da hukuncin, suna mai cewa zai taimaka wajen dakile irin waɗannan munanan laifuka.
Masu ruwa da tsaki sun kuma yi kira ga iyaye da al’umma su ci gaba da kai rahoton duk wani nau’in cin zarafi domin tabbatar da an hukunta masu laifi tare da kare yara daga irin waɗannan abubuwa.
