Atiku ya bukaci magoya bayan ADC su kwantar da hankalin su

0
Atiku ya bukaci magoya bayan ADC su kwantar da hankalin su

Atiku ya bukaci magoya bayan ADC su kwantar da hankalin su

Spread the love

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya buƙaci magoya bayan jam’iyyar ADC da su kwantar da hankalinsu, yana mai jaddada cewa hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara bai soke zaɓen fidda gwani da ya ba shi tikitin takarar shugaban ƙasa ba. Ya ce babu dalilin da zai sa jam’iyyar ta firgita.

Atiku ya bayyana cewa hukuncin kotun ya shafi rikicin shugabancin jam’iyyar ne kawai, ba kuma ya shafi sahihancin ‘yan takarar da suka fito ta hanyar zaɓen fidda gwani ba. Ya zargi wasu da yaɗa bayanan ƙarya domin tayar da hankali a cikin jam’iyyar.

Ya ce ADC ta umarci lauyoyinta su ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Koli domin neman hukunci na ƙarshe, yana mai tabbatar da cewa jam’iyyar za ta ci gaba da bin hanyoyin doka wajen kare haƙƙinta.

Atiku ya kuma yi kira ga magoya bayan jam’iyyar su ci gaba da haɗa kai da kuma mayar da hankali kan shirye-shiryen zaɓen shekarar 2027, yana mai cewa jam’iyyar na da cikakken yaƙinin samun nasara duk da ƙalubalen shari’ar da take fuskanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *