Babu maganin sabuwar nau’in cutar Ebola zuwa yanzu – Ministan Lafiya

0
Babu maganin sabuwar nau'in cutar Ebola zuwa yanzu - Ministan Lafiya

Babu maganin sabuwar nau'in cutar Ebola zuwa yanzu - Ministan Lafiya

Spread the love

Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama’a na Najeriya, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya bayyana cewa har yanzu babu wani takamaiman magani ko allurar rigakafin cutar Ebola ta nau’in Bundibugyo da aka amince da amfani da su a hukumance.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce masana na ci gaba da gudanar da bincike domin gano hanyoyin da za su taimaka wajen magance cutar.

Ali Pate ya ce majinyaciyar da aka tabbatar tana ɗauke da cutar a Abuja tana samun kulawar likitoci, ciki har da magungunan tallafa wa jiki wajen yaƙi da cutar.

Ya bayyana cewa an ba ta wasu magunguna a matakai daban-daban na jinyarta, saboda da farko ana zargin tana fama da wata cuta mai alaƙa da ƙwayoyin cuta, kafin a tabbatar da cewa Ebola ce ta kama ta.

Ministan ya ce a lokacin hirar, majinyaciyar tana cikin kwanciyar hankali, amma ya yi gargaɗin cewa yanayin masu fama da irin wannan cuta na iya sauyawa yayin da cutar ke ci gaba.

Ya kuma bayyana cewa kayan aikin gwaje-gwaje, ƙwararrun ma’aikatan lafiya da tsarin kula da marasa lafiya a Najeriya sun taimaka wajen gano cutar da kuma fara ɗaukar matakan shawo kanta.

Ya ƙara da cewa hukumomin lafiya na ci gaba da bin diddigin mutanen da suka yi hulɗa da majinyaciyar domin hana yaɗuwar cutar, tare da kira ga ‘yan Najeriya da su bi umarnin hukumomi.

Cutar Ebola na iya yaɗuwa ta hanyar taɓa jini ko wasu ruwan jikin wanda ya kamu da ita, ko kuma kayan da suka gurɓata.

Hukumomi sun buƙaci jama’a da su guji hulɗa da waɗanda ake zargin suna ɗauke da cutar tare da kai rahoton duk wata alama da ta tayar da hankali ga jami’an lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *