Majalisar Dokokin Kano ta gayyaci wani Dan Majalisa bisa zargin yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf ba’a da Zomo
Majalisar Dokokin Kano ta gayyaci wani Dan Majalisa bisa zargin yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf ba'a da Zomo
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta mika dan majalisar da ke wakiltar mazabar Nasarawa, Yusuf Bello-Aliyu, ga kwamitin ladubba da da’a na majalisar domin bincike kan zargin yin kalaman da ake ganin sun yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf ba’a.
Matakin ya biyo bayan wani rubutu da bidiyonsa suka bazu a kafafen sada zumunta.
Dan majalisar mai wakiltar jam’iyyar NNPP ya shiga cikin ce-ce-ku-ce bayan dan majalisa mai wakiltar mazabar Minjibir, Abdulhamid Abdul-Minjibir na jam’iyyar APC, ya gabatar da kudirin gaggawa a zaman majalisar.
Abdul-Minjibir ya bayyana cewa ya ga wani bidiyo da ake zargin Bello-Aliyu yana rike da kunnuwan zomo tare da furta kalaman da ya yi imanin ba su dace da matsayin dan majalisa ba.
Abdul-Minjibir ya jaddada cewa ya kamata masu rike da mukaman majalisa su kasance abin koyi ga al’umma, tare da kiyaye mutuncin mukamansu.
Ya ce abin da ya gani a bidiyon ya ba shi mamaki, lamarin da ya sa ya bukaci a mika batun ga kwamitin da’a domin gayyatar dan majalisar ya yi bayani kan abin da ya faru.
A nasa bangaren, wasu ‘yan majalisar sun nuna damuwarsu kan yadda ake amfani da kafafen sada zumunta wajen yada kalaman cin mutunci, tare da kira da a dauki matakan da suka dace bisa dokokin majalisar.
Kakakin majalisar, Jibril Ismail-Falgore, ya amince da mika batun ga kwamitin da’a domin gayyatar Bello-Aliyu ya bayyana matsayinsa, kafin a yanke hukuncin da ya dace.
