ASUU ta yi barazanar tafiya yajin aiki kan rashin aiwatar da yarjejeniyar 2025
ASUU ta yi barazanar tafiya yajin aiki kan rashin aiwatar da yarjejeniyar 2025
Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), shiyyar Yola, ta buƙaci gwamnatocin jihohi da su gaggauta aiwatar da yarjejeniyar 2025 da aka cimma tsakanin Gwamnatin Tarayya da ƙungiyar, tana mai gargaɗin cewa rashin yin hakan na iya jawo sabon yajin aikin malamai.
Da yake jawabi ga manema labarai a Yola, Kodinetan ASUU na shiyyar, Kwamared Dani Mamman, ya ce jami’o’in gwamnati na ci gaba da fuskantar matsaloli sakamakon gazawar gwamnatocin jihohi wajen cika alƙawuran da suka ɗauka ga ƙungiyar.
Ya bayyana cewa har yanzu ba a aiwatar da biyan Consolidated Academic Tools Allowance (CATA), Professional Allowance da Earned Academic Allowance (EAA) ga malaman Jami’ar Jihar Adamawa da ke Mubi, Jami’ar Jihar Borno, Jami’ar Jihar Taraba da ke Jalingo, da kuma Jami’ar Jihar Yobe da ke Damaturu.
ASUU ta ce malamai a waɗannan jami’o’i na gudanar da dukkan ayyukan koyarwa, bincike da hidimomin jami’a kamar sauran takwarorinsu, amma ana ci gaba da hana su haƙƙoƙinsu, lamarin da ke haifar da rashin jin daɗi da kuma barazana ga zaman lafiyar tsarin ilimin jami’a.
Ƙungiyar ta buƙaci a gaggauta aiwatar da yarjejeniyar 2025, a biya dukkan kuɗaɗen alawus da ake bin malamai, tare da mutunta yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin ƙwadago, tana mai jaddada cewa idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, za ta ɗauki matakin da ya dace domin kare muradun mambobinta.
