Tinubu ya sauya tsarin INEC tare da naɗa sabbin Kwamishinoni shida gabanin zaɓen 2027
Tinubu ya sauya tsarin INEC tare da naɗa sabbin Kwamishinoni shida gabanin zaɓen 2027
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sabbin mutane shida zuwa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), domin cike guraben da suka samu sakamakon ƙarewar wa’adin wasu jami’an hukumar, gabanin babban zaɓen ƙasar na shekarar 2027.
Waɗanda aka naɗa sun haɗa da Farfesa Mustapha Aliu, wanda zai wakilci Arewa maso Yamma, da Bashir Muhammed Umar, wanda zai wakilci Arewa ta Tsakiya.
Haka kuma, an zaɓi Oluwatoyin Babalola, wadda ke riƙe da muƙamin kwamishiniyar zaɓe a Jihar Osun, domin wakiltar Kudu maso Yamma a matsayin kwamishiniyar ƙasa.
Baya ga haka, Tinubu ya sake naɗa Dakta Bala Bila a matsayin kwamishinan ƙasa mai wakiltar Arewa maso Gabas.
Haka kuma, ya zaɓi Dakta Samuel Akinjide Akinleye, tsohon babban sakatare, a matsayin kwamishinan zaɓe na mazaunin Jihar Ekiti, yayin da Zahradden Basiru Sanusi daga Jihar Jigawa zai maye gurbin Farfesa Saidu Ahmed Babura.
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa naɗe-naɗen za su fara aiki ne bayan Majalisar Dattawa ta tantance tare da tabbatar da su.
Tinubu ya buƙaci majalisar ta gaggauta tantance waɗanda aka naɗa domin cike guraben kafin babban zaɓen da ake sa ran gudanarwa a watan Janairun 2027.
