Sarki Sanusi II ya buɗe sabuwar hanyar zuba jari mai bin Ƙa’idojin Musulunci a Kano
Sarki Sanusi II ya buɗe sabuwar hanyar zuba jari mai bin Ƙa’idojin Musulunci a Kano
Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya buƙaci ’yan Najeriya, musamman ’yan kasuwa da masu harkokin kuɗi, da su faɗaɗa hanyoyin zuba jarinsu maimakon dogaro da asusun ajiya da na karɓar lamuni kawai.
Sarkin ya bayyana cewa amfani da hanyoyin zuba jari da suka dace da ƙa’idojin Musulunci, tare da inshora, na iya taimaka wa mutane wajen kare dukiyoyinsu da samar da arziki mai ɗorewa.
Sanusi ya yi wannan kira ne yayin ƙaddamar da asusun zuba jari na UTLAM Halal Fund, tare da buɗe ofisoshin kamfanin UTL Trust Management Services Limited da UTL Asset Management Limited a Kano.
Asusun zai bai wa masu zuba jari damar saka kuɗaɗensu a fannoni daban-daban da aka zaɓa bisa ƙa’idojin Shari’ar Musulunci, ƙarƙashin kulawar ƙwararru.
Sarkin ya bayyana cewa wasu ’yan kasuwa a Kano sun yi asarar dukiyoyi masu yawa sakamakon gobara, sata da zagon ƙasa, inda wasu ma suka rufe kasuwancinsu saboda rashin isassun hanyoyin samun taimakon kuɗi domin farfaɗowa.
Ya ce amfani da kayayyakin kuɗi da suka dace da koyarwar Musulunci na iya taimaka wa ’yan kasuwa wajen kare kadarorinsu da inganta tsaron dukiyoyinsu.
A nasa jawabin, shugaban kamfanin UTL, Dakta Shamsuddeen Usman, ya ce buɗe ofishin Kano na da nufin kusantar da ayyukan kamfanin ga al’umma, ba wai kawai ƙara yawan rassansa ba.
Ya ƙara da cewa ofishin zai samar da ayyukan kula da amana da kadarori, rubuta wasiyya da sauran hanyoyin zuba jari da suka dace da Shari’ar Musulunci, domin hidima ga daidaikun mutane da hukumomi a Kano da sauran jihohin Arewacin Najeriya.
