Ƴan sanda sun kama mutum uku da ake zargi da ta’addancin Shilla a Adamawa
Rundunar ’yan sandan jihar Adamawa ta sanar da kama wasu mutane uku da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, ciki har da wasu biyu da ake zargin mambobin kungiyar ‘yan daba ta Shilla ne, a wasu samame da aka gudanar a kananan hukumomin Yola ta Arewa da Yola ta Kudu.
Rundunar ta bayyana cewa kamen na daga cikin matakan da take dauka domin dakile ayyukan bata-gari da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.
A cewar rundunar, an kama Abdulmalik Mohammed mai shekaru 22 a ranar 12 ga Yuni bayan da ake zarginsa da kai wa wani fasinja hari a cikin adaidaita sahu a yankin Doubeli Bye-Pass tare da kwace masa wayar salula da amfani da adda.
Bayan wanda abin ya shafa ya yi ihu neman taimako, wasu jama’a ne suka cafke wanda ake zargin kafin jami’an ’yan sanda su karbe shi domin gudanar da bincike.
Binciken farko ya nuna cewa ana zargin mutumin da hannu a wasu sace-sace da suka faru a cikin garin Yola, ciki har da satar injin dinki a Tsohon Kasuwa.
Rundunar ta ce tana ci gaba da bincike domin gano sauran mutanen da ake zargi suna da alaka da wadannan laifuka.
A wani samame na daban kuwa, jami’an ’yan sanda sun kama Abba Abdullahi mai shekaru 17 da Abdulrahman Saidu mai shekaru 16, wadanda ake zargin mambobin kungiyar Shilla ne.
An ce an same su da muggan makamai da suka hada da wukake, wadanda ake zargin sun shirya amfani da su wajen aikata laifi a wani bikin murnar zagayowar ranar haihuwa.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Kabir Umar Hassan, ya yabawa jami’an da suka gudanar da aikin tare da jaddada kudirin rundunar na murkushe kungiyoyin bata-gari da ke barazana ga zaman lafiyar al’umma.
