Gwamnatin Najeriya ta fara shari’ar Ɗaruruwan wadanda ake zargi da ta’addanci a Abuja

0
20260615_175229
Spread the love

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta fara wani sabon zagaye na shari’ar ɗaruruwan mutane da ake zargi da aikata laifukan ta’addanci a babban birnin tarayya Abuja.

An gudanar da shari’un ne a kotunan Babbar Kotun Tarayya daban-daban, yayin da aka tsaurara matakan tsaro a harabar kotun da kewayenta domin tabbatar da zaman lafiya yayin gudanar da shari’ar.

Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, shi ne ke jagorantar tawagar masu gabatar da ƙara tare da Daraktan Gurfanar da Ƙara na Tarayya, Rotimi Oyedepo.

Wadanda ake tuhuma na fuskantar zarge-zargen ta’addanci, ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci da kuma taimakawa masu tayar da ƙayar baya.

Rahotanni sun nuna cewa sama da mutum 400 ne aka gurfanar a wannan sabon zagaye na shari’a, wanda ke daga cikin matakan da gwamnati ke ɗauka domin hanzarta hukunta masu hannu a ayyukan ta’addanci da kuma ƙarfafa yaƙi da rashin tsaro a ƙasar nan. An kuma samar da lauyoyi ga waɗanda ba su da hali ta hannun Hukumar Ba da Agajin Shari’a ta Najeriya.

Wannan mataki na zuwa ne yayin da gwamnati ke ƙara matsa kaimi wajen gurfanar da waɗanda ake zargi da alaƙa da ƙungiyoyin ta’addanci, tare da nuna aniyarta ta tabbatar da cewa an yi adalci cikin gaggawa ga duk wanda aka samu da laifi ko kuma aka wanke daga zargi bisa hujjojin da kotu ta amince da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *