Zaɓen 2027: Peter Obi ya yi alkawarin sakin Nnamdi Kanu idan ya zama shugaban kasa

0
Zaɓen 2027: Peter Obi ya yi alkawarin sakin Nnamdi Kanu idan ya zama shugaban kasa

Peter Gregory Obi

Spread the love

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC a zaben 2027, Peter Obi, ya bayyana cewa zai saki jagoran IPOB, Nnamdi Kanu, idan har ya samu damar zama shugaban Najeriya.

Obi ya ce babu wani dalili mai karfi da zai sa a ci gaba da tsare Kanu saboda kalaman da ya rika yi a gidan rediyon Biafra.

Da yake jawabi ga wasu ‘yan Najeriya a birnin Washington na kasar Amurka, Obi ya bayyana cewa zagi ko kiran mutane da sunaye marasa dadi ba laifi ba ne da ya kamata a daure mutum a kai.

Ya ce ‘yan siyasa sukan fuskanci irin wadannan kalamai a kai a kai, don haka bai ga hujjar ci gaba da tsare Kanu ba.

Tsohon gwamnan na Anambra ya kara da cewa idan ya zama shugaban kasa, zai rungumi tattaunawa da dukkan masu neman sauyi ko masu korafi a sassan kasar nan domin gano matsalolinsu da kuma samar da mafita ta lumana maimakon amfani da karfi.

Kalaman Obi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan makomar Kanu da kuma yadda gwamnati za ta tunkari matsalar masu rajin kafa Biafra.

Wannan matsaya tasa na iya kara jawo ce-ce-ku-ce a fagen siyasar Najeriya gabanin babban zaben shekarar 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *