Galadima ya kai ziyarar ta’aziyya ga Lamido Funange kan rasuwar shugaban karamar hukumar Fufore
Galadima ya kai ziyarar ta’aziyya ga Lamido Funange kan rasuwar shugaban karamar hukumar Fufore
Ɗan takarar gwamnan Jihar Adamawa a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Ahmed Galadima Aminu, ya jagoranci tawaga zuwa fadar Lamidon Funnange, Alhaji Sani Ahmadu Ribadu, domin miƙa ta’aziyya kan rasuwar shugaban Ƙaramar Hukumar Fufore, Dakta Yahaya Saidu.
Tawagar ta ƙunshi abokin takarar mataimakin gwamna na Galadima, Hon. Adamu Kamale, wasu mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar Adamawa, ɗan takarar sanatan Adamawa ta tsakiya na APC, Comrade Mustapha Salihu, da wasu manyan jami’an kwamitin yaƙin neman zaɓensa.
A yayin ziyarar, Galadima ya bayyana rasuwar Dakta Saidu a matsayin babban rashi ga iyalansa, al’ummar Fufore da jihar baki ɗaya.
Lamidon Funnange ya gode wa Galadima da tawagarsa bisa nuna damuwa da goyon baya ga masarautar da al’ummar yankin a wannan lokaci na alhini.
Bayan haka, Galadima da tawagarsa sun ziyarci gidan marigayin domin miƙa ta’aziyya ga iyalansa.
Haka kuma, sun kai ziyara ga iyalan Ismaila Numan domin jajanta musu kan rasuwar uwargidansu, Hajiya Aishatu Kingi.
Tawagar ta yi addu’ar Allah ya gafarta wa mamatan, ya ba su Aljannatul Firdaus, sannan Ya ba iyalansu haƙurin jure wannan babban rashi.
