Sojoji sun hallaka ’yan Boko Haram 25 bayan dakile hari a sansanin sojoji a Borno

0
 ’Sojoji sun hallaka ’yan Boko Haram 25 bayan dakile hari a sansanin sojoji a Borno

Sojoji sun hallaka ’yan Boko Haram 25 bayan dakile hari a sansanin sojoji a Borno

Spread the love

Dakarun Sojin Najeriya da ke ƙarƙashin Operation Hadin Kai sun dakile wani hari da mayakan Boko Haram suka kai kan wani sansanin sojoji a Jihar Borno.

Rundunar ta ce dakarun sun yi artabu da maharan tare da tilasta musu ja da baya bayan da suka kasa kutsawa cikin sansanin.

Rahotanni sun bayyana cewa harin ya kasance wani yunƙuri na kai farmaki kan wuraren da sojoji ke jibge, amma dakarun sun mayar da martani cikin gaggawa, inda suka yi amfani da ƙarfin wuta wajen tarwatsa maharan. An ce harin ya haifar da asarar rayuka a tsakanin ’yan ta’addan.

A cewar rahoton, kimanin mayakan Boko Haram 25 ne aka kashe yayin arangamar, yayin da wasu daga cikin maharan suka tsere da raunuka.

Dakarun sun kuma samu nasarar kwato wasu makamai da alburusai bayan fatattakar ’yan ta’addan.

Rundunar Sojin ta ci gaba da gudanar da ayyukan share fage da bincike a yankin domin gano inda sauran ’yan ta’addan suka tsere tare da hana sake kai irin wannan hari.

Hare-haren na daga cikin ci gaba da ayyukan sojoji na murƙushe ayyukan Boko Haram da ISWAP a yankunan Arewa maso Gabashin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *