Majalisar wakilai ta bukaci INEC ta hana ’yan takara da sunayensu ba ya cikin rajistar jam’iyya
Majalisar wakilai ta bukaci INEC ta hana ’yan takara da sunayensu ba ya cikin rajistar jam’iyya
Kwamitin Majalisar Wakilai mai kula da harkokin zaɓe ya buƙaci Independent National Electoral Commission (INEC) ta hana duk wani ɗan takara shiga zaɓen 2027 idan ba a samu sunansa cikin rajistar mambobin jam’iyyar da ta tsayar da shi ba.
Kwamitin ya ce matakin ya zama wajibi domin tabbatar da bin tanadin Sashe na 77 na Dokar Zaɓe ta 2026.
Shugaban kwamitin, Bayo Balogun, ya bayyana hakan cikin wata wasiƙa da ya aika wa INEC, inda ya buƙaci hukumar ta gudanar da cikakken bincike kan sunayen ‘yan takarar da dukkan jam’iyyun siyasa suka gabatar domin zaɓen 2027.
Ya ce dole ne a tabbatar da cewa sunayen ‘yan takarar suna cikin rajistar mambobin jam’iyyunsu da aka gabatar wa INEC a lokacin da doka ta tanada.
Wannan buƙata ta biyo bayan hukuncin Kotun Ƙoli da ya dawo da wasu muhimman tanade-tanaden Sashe na 77 na Dokar Zaɓe ta 2026, ciki har da waɗanda suka shafi rajistar mambobin jam’iyyu da gudanar da zaɓen fidda gwani.
Kotun ta bayyana cewa tanade-tanaden ba su saɓa wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ba.
Kwamitin ya ce aiwatar da dokar zai taimaka wajen hana rikice-rikicen shari’a da ka iya tasowa bayan zaɓen fidda gwani. Ya kuma buƙaci INEC ta fara aiwatar da tanade-tanaden dokar ba tare da bata lokaci ba, yana mai cewa hakan zai zama gwaji ga hukumar wajen tabbatar da cewa jam’iyyu da ‘yan takararsu sun bi dokokin zaɓe gabanin babban zaɓen 2027.
