Gwamnonin Arewa maso Gabas sun cimma sabbin matakai kan tsaro, sufuri da wutar lantarki
Gwamnonin Arewa maso Gabas sun cimma sabbin matakai kan tsaro, sufuri da wutar lantarki
Gwamnonin jihohin Arewa Maso Gabas sun gudanar da taronsu na 13 a Maiduguri, inda suka tattauna kan tsaro, tattalin arziki, ilimi, makamashi da sauran batutuwan da suka shafi ci gaban yankin.
Taron ya samu halartar gwamnonin Borno, Adamawa da Gombe, yayin da mataimakan gwamnonin Bauchi da Yobe suka wakilci gwamnoninsu.
Gwamnonin sun yabawa Gwamnatin Tarayya kan kulawar da ta kara bai wa yankin, musamman ayyukan layin dogo na Port Harcourt–Jos–Bauchi–Gombe–Maiduguri da babbar hanyar Akwanga–Jos–Bauchi–Gombe–Biu–Maiduguri. Sun kuma bukaci a farfado da ayyukan hako mai da suka tsaya a Magumeri da Gubio na Jihar Borno.
A bangaren makamashi da sufuri, kungiyar ta amince da fadada tashoshin CNG da LNG a yankin domin rage tsadar sufuri, tare da shirin kafa zirga-zirgar jiragen sama na yankin.
Gwamnonin sun kuma marabci samar da babura masu kafa uku 10,000 masu amfani da wutar lantarki, bas 10 da motocin haya 300 da tallafin NEDC.
Game da tsaro, kungiyar ta yaba wa jami’an tsaro kan nasarorin da aka samu wajen yaki da ‘yan ta’adda, amma ta ce har yanzu akwai kalubalen jin kai da na ababen more rayuwa.
Ta jaddada bukatar kara hadin gwiwar jihohi, musayar bayanan sirri da shiga cikin al’umma domin dakile sabbin barazanar tsaro.
Gwamnonin sun kuma jaddada muhimmancin bai wa matasa ingantaccen ilimi, koyon sana’o’i, fasahar zamani da guraben aikin yi.
Sun kuma amince da hadin gwiwa wajen kare muhalli da rage sare itatuwa, yayin da aka tsara gudanar da taron kungiyar na gaba a ranakun 18 da 19 ga Disamba 2026 a Gombe.
