Ban ba da umarnin kama matasa masu sanye da rigar ‘Tinubu Must Go’ ba – Zulum

0
Babagana Umara Zullum
Spread the love

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce bai taɓa bayar da umarnin kama masu adawa da jam’iyyar APC ko waɗanda ke sukar gwamnatinsa ba.

Zulum ya bayyana hakan ne a Maiduguri ranar jumma’a, yayin da yake martani kan kamen wasu mutane sanye da rigunan da ke ɗauke da rubutun “Tinubu Must Go”, lamarin da ya ce ya ba shi mamaki.

Gwamnan ya ce hankalinsa ya fi karkata ne wajen dawo da zaman lafiya da sake gina Borno bayan tashe-tashen hankulan Boko Haram, maimakon kama abokan hamayyarsa na siyasa.

Ya kuma bayyana cewa tun bayan da aka fara samun nasarar dawo da zaman lafiya, gwamnatinsa ta mayar da hankali kan sake tsugunar da waɗanda suka rasa matsugunansu, sake gina al’ummomin da rikici ya lalata da kuma samar da makarantu da asibitoci.

A gefe guda kuma, rundunar ’yan sandan Borno ta ce mutanen biyar da aka kama a Maiduguri ba wai saboda sanya rigar “Tinubu Must Go” kaɗai aka kama su ba.

’Yan sandan sun ce an same su da wasu abubuwa da ake zargin sun haɗa da tabar wiwi, ƙwayoyi, kwalbar shisha da almakashi, sannan aka gurfanar da su a gaban kotu bisa zarge-zargen haɗa baki, tayar da tarzoma, dagula zaman lafiya da daba.

Sai dai lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce daga wasu ’yan adawa da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam, waɗanda ke ganin ya kamata a kare ’yancin faɗar ra’ayin siyasa.

Zulum kuwa ya ce wasu daga cikin masu sukar gwamnatinsa na yin hakan ne yayin da zaɓen 2027 ke ƙara matsowa, yana mai cewa irin waɗannan zarge-zargen ba za su hana gwamnatinsa ci gaba da ayyukan sake gina Borno ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *