Dino Melaye ya ce ana ci gaba da tattaunawa domin hadakar yan adawa kamin zaɓen 2027
Dino Melaye ya gargaɗi ’Yan Najeriya kan karin tsanantar yunwa idan Tinubu ya ci Zaɓen 2027
Jigo a jam’iyyar ADC, Dino Melaye, ya bayyana cewa ana ci gaba da tattaunawa tsakanin ’yan adawa kan yiwuwar kafa hadaka gabanin zaben shugaban kasa na 2027.
Melaye ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya yi wani rubutun mai take n: “Coalition talk is on. Tinubu must go.”
Ya ce tattaunawar na da alaka da kokarin hada kan jam’iyyun adawa da masu ruwa da tsaki domin samar da wata babbar kungiya da za ta fafata da jam’iyyar APC a zaben 2027.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tuntubar juna tsakanin wasu jam’iyyun adawa kan yadda za su hada karfinsu.
Rahoton ya ce shirin hadakar na da alaka da kokarin kungiyar G100, wadda ta yi kira ga jam’iyyun adawa da su fifita muradun kasa da samar da tsari guda na siyasa.
Wasu daga cikin jam’iyyun da aka ce suna cikin tattaunawar sun hada da ADC, NDC, wani bangare na PDP, APM, PRP da SDP.
An kuma gudanar da wani taron ’yan adawa a Abuja a ranar 31 ga Agusta, inda aka tattauna kan yiwuwar samar da hadakar siyasa gabanin 2027.
Sai dai wasu fitattun ’yan siyasa, ciki har da Atiku Abubakar, Peter Obi, Rabiu Kwankwaso da Rotimi Amaechi, ba su halarci taron ba, yayin da tattaunawar hadakar ke ci gaba.
