Sabon kwamishinan ‘yan sanda na Adamawa ya ziyarci AIG na Shiyya ta 3
Ofishin AIG Police zone 3
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Adamawa, CP Kabir Umar Hassan, ya kai ziyarar girmamawa ga Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda mai kula da Shiyya ta 3, AIG Akinwale Kunle Adaniran, a hedikwatar shiyyar.
Ziyarar na da nufin ƙarfafa haɗin kai da inganta dabarun aikin ‘yan sanda a yankin.
A yayin ganawar, AIG ya buƙaci sabon Kwamishinan da ya jajirce wajen nuna ƙwarewa a aikinsa.
A nasa ɓangaren, CP Kabir ya tabbatar da biyayyarsa da kuma jajircewarsa wajen inganta tsaro a Jihar Adamawa.
