Tuggar ya yi murabus a gwamnatin Tinubu
Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar
Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, ya yi murabus daga mukaminsa a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Rahotanni sun nuna cewa ya ajiye aikin ne domin mayar da hankali kan shirinsa na siyasa, musamman yiwuwar tsayawa takarar gwamna a Jihar Bauchi a 2027.
Ana sa ran fadar shugaban ƙasa za ta sanar da wanda zai maye gurbinsa nan gaba kaɗan.
