Rikici ya barke yayin da EFCC ta mamaye gidan Malami a Abuja
Jami'an EFCC sun mamaye gidan Malami a Abuja
Jami’an hukumar EFCC ɗauke da makamai sun mamaye gidan tsohon Ministan Shari’a na Tarayya, Abubakar Malami, da ke Abuja, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce.
Rahotanni sun ce jami’an sun isa gidan ne cikin motoci da dama, inda suka kewaye wurin tare da hana zirga-zirga, yayin da wasu ke cewa sun kai samamen ne domin karbar iko da kadarar Malami.
A cewar rahotanni, wannan mataki na zuwa ne bayan wata takaddamar da ta barke tsakaninsa da jami’an hukumar a ranar litinin, inda Malami ya nemi a nuna masa umarnin kotu kafin a yi masa alama a gidan nasa.
Wannan lamari yana da alaƙa da binciken da ake yi kan wasu kadarori da ake zargin suna da nasaba da aikata laifuka, inda wata kotu a baya ta bayar da umarnin kwace kadarori da dama da ake zargi suna da alaƙa da Malami da ‘ya’yansa.
Sai dai Malami ya shaida cewa matakin da EFCC ke ɗauka na iya zama ƙoƙarin muzanta shi, yana mai jaddada cewa har yanzu shari’ar tana gaban kotu kuma ba a kammala ta ba.
