Sojoji sun hallaka ‘yan bindiga a maboyar Bello Turji

0
Troops-1024x768
Spread the love

Rundunar sojojin Najeriya ta kai farmaki kan maboyar fitaccen shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji, inda ta kashe ‘yan bindiga da dama bayan artabu mai tsanani.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi arangama mai ƙarfi tsakanin sojoji da ‘yan bindigar, kafin daga bisani sojojin su samu nasarar murƙushe su tare da tarwatsa sansanoninsu.

Harin na daga cikin matakan da jami’an tsaro ke ɗauka domin kawo ƙarshen ayyukan ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma da kuma dawo da zaman lafiya.

An buƙaci al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *