Gwamnatin Kano ta bayar da tallafi ga fursunoni domin bikin Eid Al fitr

0
1000473730
Spread the love

Kano, Najeriya – Gwamnatin Jihar Kano ta raba kayan tallafi ga fursunoni a dukkan cibiyoyi 13 na jihar domin shirya bukukuwan Eid al-Fitr.

Tallafin sun haɗa da shanu 14, buhunan shinkafa 82 mai nauyin kilo 50 kowanne, kwalaben man girki 38 na kilogiram 25, da kayan miya daban-daban.

Shugabar kwamitin kula da ayyuka n jinkai, Hajiya Azumi Namadi Bebeji, ta mika saƙon a madadin Gwamnati, tana kira ga fursunonin da su yi addu’o’i domin zaman lafiya, haɗin kai, da ci gaba a jihar da ƙasa baki ɗaya, tare da kasancewa masu bin doka.

Tallafin ya nuna yadda gwamnati ke kulawa da rayuwar fursunoni da kuma ƙarfafa jin kai da haɗin kai a al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *