Zan kare kaina, ban yi nadama ba – Malami
Abubakar Malami, tsohon ministan Shari'ar Najeriya
Tsohon ministan shari’a kuma babban lauyan tarayya, Abubakar Malami, ya ce bai da wata nadama kan ayyukan da ya yi a lokacin da yake kan mulki.
Ya bayyana cewa duk matakan da ya ɗauka sun kasance ne bisa doka, yana mai jaddada cewa bai aikata wani abu da zai sa ya ji nadama ba.
Malami ya kuma ce a shirye yake ya kare kansa daga duk wasu zarge-zarge da ake masa, tare da nuna cikakken yakini cewa gaskiya za ta bayyana ta hanyar shari’a.
