Malamin addini ya saɓa umarnin Sarkin Musulmi a Sokoto
Sheikh Musa Lukuwa, Sokoto
Wani malamin addinin Musulunci a Jihar Sokoto ya jagoranci sallar Idi tare da mabiyansa duk da umarnin Sarkin Musulmi na jinkirta bikin, sakamakon rashin ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa malamin ya dogara ne da bayanan ganin wata daga Jamhuriyar Nijar, wanda ya tabbatar masa da shigowar watan Shawwal, shi ya sa ya yanke shawarar gudanar da sallar Idi a ranar.
Wannan mataki ya haifar da cece-kuce a tsakanin al’umma, inda wasu ke ganin ya yi daidai bisa hujjar addini, yayin da wasu ke sukar matakin tare da cewa ya saɓa wa umarnin shugabancin addini, wanda ya kamata a bi domin tabbatar da haɗin kai da kauce wa rikice-rikice.
