Burtaniya za ta rufe hanyoyi da hana shawagin jirage saboda ziyarar Tinubu
Gwamnatin Burtaniya ta sanar da daukar wasu tsauraran matakan tsaro a garin Windsor domin shirye-shiryen karbar bakuncin shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.
Ana sa ran shugaban zai kai ziyara ta musamman a kasar tare da matarsa Oluremi Tinubu.
‘Yan sandan Thames Valley sun bayyana cewa za a hana duk wani jirgi ko jirgi marar matuki shawagi a sararin samaniya da ke kusa da Windsor Castle daga karfe 7:00 na safe zuwa 11:59 na dare ranar 18 ga Maris, da kuma takaita ajiye motoci a wasu wurare.
Sauran matakan da za a dauka domin tabbatar da tsaro sun haɗa da jibge jami’an tsaro da dama a wurare daban-daban da kuma yin amfani da kyamarorin CCTV da wasu na’urorin tsaro.
Wadannan matakai za su fara aiki tun daga 17 ga Maris, kwana guda kafin zuwan shugaban, kumahukumomi sun yi gargadin hukunta duk wanda ya saɓa wa dokokin.
