Shugaba Tinubu ya nada Oyedele a matsayin karamin Ministan kudi
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Taiwo Oyedele a matsayin karamin ministar kudi na Najeriya, inda ya maye gurbin Dr Doris Anite-Uzoka.
Anite-Uzoka yanzu za ta koma Ma’aikatar Kasafin Kudi da Tsare-tsare ta kasa, a matsayin ƙaramar Minista.
Shugaba Tinubu ya mika sunan Oyedele ga Majalisar Dattawa don tabbatarwa a cikin wata wasika da ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.
Oyedele daga Ikaram, Akoko, Jihar Ondo, shi ne shugaban Kwamitin Shugaban Kasa kan Manufofin Kudi da Gyaran Haraji, wanda ya gyara tsarin haraji na Najeriya.
