Ƴan shi’ar Najeriya sun yi zanga-zangar nuna goyon bayan Iran

0
20260302_152455
Spread the love

Ƙungiyar mabiya aƙidar Shi’a ta Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky, ta gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayanta ga jamhuriyar Musulunci ta Iran saboda hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa ƙasar.

Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce mabiyanta sun gudanar da zanga-zangar a biranen Abuja da Zariya da Illela da Kaduna da Kano da Jigawa da Bauchi da Azare da Potiskum da Minna da Katsian da Yola da sauransu.

Ƙungiyar ta ce ta kuma riƙa gudanar da addu’o’in neman nasara ga Iran.

Haka ma ƴan ƙungiyar sun ce sun jajanta wa al’ummar Musulman duniya, musamman Iraniyawa kan mutuwar jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *