Gwamna Fintiri ya yi Alla-wadai da harin Boko Haram a jihar Adamawa

0
1772115669241
Spread the love

Gwamna Ahmadu Fintiri ya ziyarci ƙauyen Kirchinga a ƙaramar hukumar Madagali, jihar Adamawa, bayan harin da mayaƙan Boko Haram suka kai kwanan nan.

Gwamnan, tare da manyan jami’an gwamnati da na tsaro, ya kai ta’aziyya ga iyalan da abin ya shafa.

Fintiri ya ce gwamnati za ta ci gaba da daukar dukkan matakan da suka dace don kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da tabbatar da cewa waɗanda ke kai hare-hare basuyi bacci ido rufe ba.

Ya kuma jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin jami’an tsaro da al’umma wajen dakile ayyukan ta’addanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *