Dalung ya yi Alla-wadai da kashe wasu matafiya a Filato

0
20260225_120223
Spread the love

Tsohon ministan matasa da wasanni a Najeriya, Solomon Dalong ya yi Alla-wadai da kisan gillar da aka yi wasu mutane a baya-bayan nan a sassan jihar Filato, inda ya ce ya yi imanin cewa kasar ta wuce “lokacin tare hanya da kuma kashe matafiya”.

A cikin wata sanarwa, Dalong ya bayyana kisan gillar da aka yi wa wasu matasa ‘yan kasuwa hudu a Dorowa Babuje a karamar hukumar Barakin Ladi a ranar 23 ga Fabrairu, a matsayin abin tausayi kuma abin takaici.

Ya yi takaicin cewa wadanda abin ya shafa, wadanda aka ruwaito suna kan hanyarsu ta zuwa Kasuwar Litinin ta Pankshin, a ware su ne aka kashe su.

Ya kara da cewa lamarin ya zo ne bayan wani hari da aka kai wa wani otal a cikin garin kwana daya da ta gabata inda aka ruwaito mutane tara sun rasa rayukansu.

Dalung ya kuma yi tsokaci kan rahotannin matasa makiyaya Fulani guda uku da aka ce sun ɓace kuma daga baya aka same su a mace, yana mai gargadin cewa irin waɗannan abubuwan suna ƙara rura wutar ɗaukar fansa a faɗin jihar.

Ya yi kira ga hukumomin tsaro da su tashi tsaye don ɗaukar matakai na kare rayuka da dukiyoyi tare da tabbatar da cewa an gano waɗanda ke da alhakin kisan kuma an gurfanar da su a gaban shari’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *