An sace wayoyi sama da 40 yayin da barayi suka fasa shagon caji a Adamawa
Wasu da ake zargi da fashi sun shiga wani shagon caji na waya a karamar hukumar Jada ta jihar Adamawa, inda suka sace wayoyin hannu sama da 40.
Lamarin ya faru ne a shagon Muhammad Mai Caji da ke kan hanyar zuwa Unguwar Duta’era.
Rahotanni sun bayyana cewa an yi fashin ne a lokacin da mai shagon ya je masallaci don yin sallar Isha.
An kuma ruwaito cewa wadanda ake zargin sun sace kudaden da aka samu daga cinikin (POS).
Mai shagon ya tabbatar da cewa an kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda, yana mai cewa ana daukar matakai don tuntuɓar wadanda aka sace wayoyinsu.
A halin yanzu, mazauna yankin sun bukaci hukumomin tsaro da su karfafa sintiri na dare don dakile karuwar laifukan fashi a cikin al’umma.
