APC na kan gaba a zaɓen ƙananan hukumomin Abuja

0
1000321386
Spread the love

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta fara fitar da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin Abuja, da aka gudanar a ranar Asabar.

Sakamako daga runfunan zabe na kananan hukumomi shida na babban birnin tarayya Abuja sun farasamuwa ne sa’o’i kaɗan bayan hukumar zaɓe ta INEC ta kammala gudanar da zaɓukan.

Sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi biyar daga cikin shida da ke birnin sun nuna cewa jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta lashe ƙananan hukumomi huɗu (Abaji, AMAC, Bwari, Kwali) yayin da jam’iyyar PDP ta lashe ƙaramar hukuma ɗaya (Gwagwalada) kuma ana dakon sakamakon zaɓen ƙaramar hukumar Kuje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *