Jami’an tsaro sun kama mai garkuwa da mutane a Adamawa

0
IMG-20260221-WA0011

Rundunar ƴan sandan jihar Adamawa ta kai hari mabuyar ƴan ta'adda.

Spread the love

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta wargaza maboyar wani da ake zargi da satar mutane a yankin karamar hukumar Song, inda ta kama wani wanda ake zargi tare da kwato makamai da harsasai.

A cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan, SP Suleiman Yahaya Nguroje ya fitar, aikin ya biyo bayan sace mutane biyu a karamar hukumar Song, wanda hakan ya sa Kwamishinan ‘yan sanda, CP Dankombo Morris, ya tura jami’ai da mafarauta na yankin zuwa wani aikin ceto.

‘Yan sanda sun yi artabu da masu garkuwa da mutanen a wani maboyarsu da ke Maigero, inda suka kashe wani wanda ake zargi da suna Sanda na ƙauyen Maigero, yayin da wasu suka gudu da raunukan harbin bindiga.

Masu garkuwa da mutanen sun kashe wani wanda aka yi garkuwa da shi, yayin da wani Jami in ƴan sa kai ya samu rauni.

‘Yan sanda sun kwato bindiga kirar AK-47 guda ɗaya, da harsasai 83.

Kwamishinan ‘yan sandan ya umarci Rundunar Crack Squad, Yola, da ta ɗauki nauyin binciken tare da ceto sauran wanda aka yi garkuwa da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *