Hisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a Kano
Hukumar Hisbah a jihar Kano ta ce jami’anta sun kama wasu mutum tara Musulmai a jiya Laraba a take ranar farko ta azumin watan Ramadan saboda an gan su suna cin abinci da tsakar rana.
Jihar Kano na da yawan Musulmai, inda tsarin shari’ar Musulunci ke aiki tare da dokokin ƙasa na yau da kullum.
A kowane Ramadan, Hisbah na bincika wuraren sayar da abinci da kasuwanni domin tabbatar da cewa Musulmai na bin dokokin azumi.
A wasu wurare, wurarern cin abinci na ci gaba da aiki musamman a yankunan da Kiristoci da dama ke zaune.
Ga Musulmai masu azumi, cin abinci daga fitowar rana zuwa faduwar rana haramun ne.
Yin azumi na daga cikin ginshikan Musulunci guda biyar da ke kafa yadda Musulmai ke gudanar da rayuwarsu.
