Lakurawa sun kashe aƙalla mutum 30 a Kebbi

0
1000447007
Spread the love

Wasu ‘yanbindiga da ake zargin ‘yan ƙungiyar Lakurawa ne sun kashe mutum 30 tare da lalata ƙauyuka bakwai a hare-haren da suka kai a yankin arewa maso yammacin Jihar Kebbi, kamar yadda ’yan sanda suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Alhamis.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, Bashir Usman, ya ce ’yan ƙungiyar sun kai farmakin ne a yankin Bui na ƙaramar hukumar Arewa da misalin ƙarfe 1:15 na rana a ranar Laraba.

Wani rahoton da AFP ya gani ya nuna cewa maharan sun kashe sama da mutum 30.

Usman ya ce adadin waɗanda suka mutu yana dayawa idan aka haɗa da mutanen da suka fito daga ƙauyukan Mamunu da Awasaka da Tungan Tsoho da Makangara da Kanzo da Gorun Naidal da Dan Mai Ago domin kare kansu daga harin.

Wani mazaunin ƙauyen Kanzo ya ce sun ji ƙarar bindiga suna cikin gidajensu, lamarin da ya sa mutane suka riƙa gudu domin neman mafaka, inda harsasai suka samu wasu daga cikinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *