Ribadu ya kalubalanci El-rufa’i da ya kai shaidar sayan sinadari mai guba ga DSS

0
1000537240
Spread the love

Ofishin mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya mayar da martini ga tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai wanda ya nemi bahasi kan shiga da wata guba mai haɗari cikin ƙasar.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, ya zargi ofishin mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, a ƙaƙashin jagorancin Mallam Nuhu Ribadu, da sayo kimanin kilogiram 10 na wani sinadari mai haɗari da ake kira ‘thallium sulphate’, daga ƙasar Poland.

El-Rufai ya yi wannan zargin ne a cikin wata wasiƙa da ya aike wa ofishin Ribadu, wadda kuma ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce jagororin adawar ƙasar na neman ƙarin haske game da wannan batun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *