Sanata Yaroe ya tabbatar da amincewar majalisar dattawa kan aika sakamakon ta hanyar na’ura

Sanata Binos Dauda Yaroe daga yankin Kudancin Adamawa ya bayyana cewa Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da ci gaba da aika sakamakon zabe ta na’ura a gyaran da aka yi kwanan nan na Dokar Zabe.
Sanata Yaroe ya bayar da tabbacinsa a wata hira da manema labarai a karamar hukumar Demsa yayin da yake mayar da martani kan matsayin da aka danganta wa wata kungiyar Sanatoci da suka yi jawabi a wani taron manema labarai kwanan nan a Abuja suna zargin cewa an yi magudi a cikin dokar da aka gyara wadda ta haifar da suka daga ‘yan Najeriya.
Yaroe ya fayyace cewa bangarorin biyu na Majalisar Dokoki ta Kasa sun amince da ci gaba da aika sakamakon zabe ta hanyar na’ura sabanin abin da ake hasashe a shafukan sada zumunta wanda a cewar sa labari ne da ba shi da tushe bare makama.
Ya yi ikirarin cewa, a matsayinsa na memba na Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Zabe, yana da hannu sosai a cikin sake duba Dokar Zabe ta 2022 yana mai jaddada cewa majalisun biyu na Majalisar Dokoki ta Kasa, ta hanyar hadin gwiwa na kwamitin, sun ba da shawarar a aika sakamakon zabe ta hanyar na’ura.
