Sojojin Najeriya sun ƙwato shanu daga ƴanbindiga a Katsina

0
1000522283
Spread the love

Dakarun sojojin Najeriya da ke gudanar da ayyuka a Jihar Katsina sun kwato dabbobi 529 da aka sace bayan wani ƙazamin artabu da wasu da ake zargin ‘ƴan bindiga ne a ƙaramar hukumar Ƙafur ta jihar.

Wata sanarwa da ta fito daga mukaddashin mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji Abayomi Adisa, ta bayyana cewa an yi nasarar gudanar da aikin ne sakamakon sahihan bayanan sirri da aka samu game da ayyukan ƴan bindiga a yankin da ke kusa da Kasuwan Sabo a ƙaramar hukumar ta Kafur.

Sanarwar ta ƙara da cewa binciken farko ya nuna cewa ana zargin ƴan bindigar sun kutsa yankin ne daga jihar Zamfara, a ƙarƙashin jagorancin Idi Abasu Aiki, wanda ake kyautata zaton ɗan’uwan ƙasurgumin ɗan bindigan nan ne, Ado Aliero.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *