Shettima ya buƙaci ƴan Najeriya su haɗa-kai don samar da zaman lafiya

0
1000403636
Spread the love

Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Kashim Shettima, ya yi kira ga ƴan Najeriya da su rungumi haɗin-kai da kuma zaman lafiya, saboda haɗin-kai shi ne ginshikin cigaban ƙasa.

Shettima ya bayyana haka ne yau Laraba a Jos, babban birnin jihar Plateau, lokacin da ya kai wa shugaban majalisar sarakunan jihar, Jacob Gyang Buba ziyara.

A cewar mataimakin shugaban ƙasar, ɗimbin kabilu da ake da su a Najeriya ne ya sa dole a ƙarfafa haɗin-kai maimakon rarrabuwar kawuna.

Mataimakin shugaban ƙasar wanda kuma ya je Plateau don bikin tarbar gwamnan jihar, Caleb Muftwang wanda ya koma jam’iyyar APC, ya yaba wa sarakunan gargajiya a jihar saboda koƙarinsu wajen tabbatar da kyakkyawan zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Ya ce sarakunan gargajiyar na da rawar taka wa wajen daɓɓaka dorewar zaman lafiya a al’ummomi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *