Tinubu zai tafi Turkiyya a yau Litinin

0
1000262560
Spread the love

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu zai yi tafiya a yau Litinin, 26 ga Janairu, zuwa ƙasar Turkiyya domin ziyarar aiki ta ƙasa, a wani yunkuri na ƙarfafa alaƙar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.

A cewar wata sanarwa da mai bai wa Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar a jiya Lahadi, ziyarar na da nufin faɗaɗa haɗin gwiwa a muhimman fannoni da suka haɗa da tsaro da ilimi da ci gaban al’umma da kirkire-kirkire da kuma harkar sufurin jiragen sama.

Sanarwar ta ce wannan ziyara na zuwa ne bayan ziyarar aiki da shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya kai Najeriya a ranakun 19 zuwa 20 ga Oktoba, 2021, wadda ta ƙara ƙarfafa alaƙar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.

A yayin ziyarar, ana sa ran ƙasashen biyu za su gudanar da tattaunawar siyasa da diflomasiyya kan muhimman batutuwa da suka haɗa da harkokin kuɗi, sadarwa, kasuwanci da zuba jari.

Daga cikin tawagar Shugaban Ƙasar da ke halartar tattaunawar diflomasiyyar akwai ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar da ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, SAN da ministan tsaro, Janar Christopher Musa, da Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Wakilai, Jimi Benson.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *