Gwamnan Kano zai koma jam’iyyar APC ranar Litinin

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf zai koma jam’iyyar APC, mai mulkin Najeriya a ranar Litinin 26 ga watan Janairun 2026.
A ranar Juma’a ne gwamnan ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyarsa ta NNPP, saboda abin da ya bayyana da rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar, sai dai a lokacin bai bayyana jam’iyyar da zai shiga ba.
Sai dai cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Lahadi, ya ce gwamna ya yanke shawarar komawa tsahowar jam’iyyarsa na APC bayan tuntuɓar abokan shawararsa na siyasa da sauran masu ruwa da tsaki.
Gwamnan ya bayyana APC da jam’iyyar mai cikakken tsari wajen tafiyar da gwamnati.
Abba Kabir Yusuf ya taɓa shiga APC a 2014 har ma ya tsaya takarar sanata, kodayake Kwankwaso ne ya yi takarar kujerar a lokacin.
Gwamna Abba Kabir ya ce sake komawa APC zai ƙara ƙarfafa alaƙa mai ƙarfi tsakanin gamnatin jihar da ta tarayya, wani abu da sanarwar ta ce zai samar wa jihar ci gaba da ƙarfafa tsaro da inganta ci gaban jihar.
”Haka kuma matakin zai kawo masalaha kan rikicin siyasar jihar da haɗin kai tsakanin al’ummar Kano”,
Sanarwar ta ƙara da cewa a ranar Litinin ɗin gwamnan zai karɓi katin jam’iyyar APC tare da wasu ƴan majalisar dokokin jihar 22 ciki har da kakakin majalisar, da ƴanmajalisar tarayya takwas da shugabannin ƙananan hukumomi 44.
