Tawagar ‘yanmajalisar Amurka ta isa Najeriya don bincika iƙirarin kisan Kiristoci

Tawagar ‘yanmajalisar Amurka ta isa Najeriya a yau Lahadi domin bincika gaskiyar iƙirarin yi iwa Kiristoci kisan gilla.
Nuhu Ribadu, mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro, ya ce ya gana da wakilan kuma zuwan tawagar na cikin abubuwan da suka amince da shi a tasu ziyarar da suka kai birnin Washington a watan Nuwamba.
“Tawagar ta ƙunshi ‘yanmajalisar wakilai Mario Díaz-Balart, Norma Torres, Scott Franklin, Juan Ciscomani, da Riley M. Moore,” in ji Ribadu cikin wata sanarwa a shafinsa na sada zumunta.
Kazalika, Jakadan Amurka a Najeriya Richard Mills na cikin tawagar.
Ribadu ya ce sun tattauna matakan yaƙi da ta’addanaci, da zaman lafiya a Afirka, da hanyoyin ƙarfafa ƙawancen tsaro tsakanin Najeriya da Amurka.
