Shugaban INEC ya sauka daga muƙaminsa bayan ƙarewar wa’adinsa

Shugaban hukumar zaɓen Najeriya, Farfesa Mahmood Yakubu ya sauka daga muƙaminsa tare da miƙa ragamar jagorancin hukumar ga May Agbamuche wadda za ta riƙe muƙamin a matsayin riko kafin naɗa sabon shugaba.
Farfesa Yakubu ya bayyana hakan ne ranar Talata a lokacin ganawarsa da kwamishinonin hukumar a shalkwatar zaɓen da ke Abuja.
Agbamuche ita ce wadda ta fi kowa jimawa a matsayin babbar kwamishina a hukumar zaɓen ƙasar.
Ya kuma yi kira da sauran kwamishinoni da daraktocin hukumar su bai wa Agbamuche cikakken goyon bayan kafin lokacin naɗa sabon shugaban hukumar.
A watan Oktoba 2015 ne tsohon Shugaban Najeriya Marigayi, Muhammadu Buhari ya naɗa Farfesa Yakubu a matsayin shugaban hukumar INEC, wanda ya maye gurbin Farfesa Attahiru Jega.
Haka a 2020 Muhammadu Buhari ya sake naɗa shi a karo na biyu don jagorantar hukumar a wa’adi na biyu.
Farfesa Yakubu ya jagoranci hukumar na tsawon shekara 10, tare da gudanar da manyan zabukan kasar biyu na 2019 da 2015.
