Sanata Natasha ta halarci zaman majalisar Najeriya

0
1000146429
Spread the love

A karon farko, sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ta halarci zaman zauren majalisar dattawan Najeriya, bayan dakatar da ita da aka yi na watanni shida.

A ranar Talata ne majalisar ta koma bakin aiki, bayan tsawaita lokacin komarsu da ƴan makonni.

Sai dai sanatar mai wakiltar kogi ta arewa ta halarci zaman majalisar ne wanda shugaban Majalisar, kuma abokin rikicin Natasha, Godswill Akpabio ya jagoranta.

Dakatar da ita ya janyo cece-kuce sosai a siyasar ƙasar, musamman saboda zargin cin zarafin da ta yi wa shugaban Majalisar Akpabio.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *